Mawakin barkwancin nan wato Yamu Baba tareda sababbin jarumai wato “Yar Hajiya” da “Adamsy” sun zo mana da sabuwar waka mai taken “Khadijatul Kubra”.
A wannan karon shima shugaban kamfanin 3SP kuma Daraktan dake shirya wannan wakokin barkwanci wato “Abubakar S. Shehu” ya fito a cikin wakar a matsayin Alhaji.
Kamfanin shirya fina-finai da wakokin barkwanci na 3SP International dake garin Jos ne ke daukar nauyin kawo mana wadannan wakoki domin nishadi.
Kalli faifan bidiyon daga kasa domin nishadi da bandariya.